Akalla malamai makarantun sakandare talatin ne suka samu horon kan wasanni a jahar Taraba.

Daga Sani Yarima Jalingo. A kokarin ganin an samu cigaban kwallon raga a Najeriya wata kungiya mai zaman kanta wato kungiyar raya wasanin da ilimin Al umma CSED ta shiya horo kan wasan raga na kwanaki biyu wa malamain makarantun sakandare a jahar Taraba. Horon ya gudanane tare da hadin gwiwar cibiyar ta CSED da majalisar wasanin jahar Taraba Wanda ya gudana a dandalin wasa na Jolly Nyame wanda kuma ya samu halartar sama da malamai talatin. Da yake jawabi a wurin bikin rufe horon ko odinatan CSED ta kasa Edema Fuludu ya baiyana jin dadinsa dangane da wannan horon da akayiwa malamai wanda acewarsa hakan zai taimaka ba ga jahar kadaiba harma da kasa baki daya. Edema Fuludu wanda tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar na Super Eagles ne ya kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai harma da kungiyar kwallon raga a Najeriya ta su yi dukkanin maiyiwa domin ganin an samu cigaban kwallon raga a nahiyar Afrika baki daya. Yace an gudanar da horon ne da zumar rage rashin aikinyi a tsakanin yaran mata ta hanyar wasanin da dai sauransu. Ko odinatan dai yace tun a shekara ta 2015 ne dai aka samar da kungiyar ta CSED domin ziyarta jihohi tana horan da irin wannan wasanin wanda tunin ta ziyarci jihohi irinsu Enugu, Ondo, Akwa Ibom da Bayelsa da dai sauransu. Shima anashi jawabi darectan majalisar wasannin jahar Taraba George Shitta ya yabawa ko odinatan Kungiyar ta CSED bisa wannan na mijin kokari da sukayi na horan da malamai makarantu sakadare dake fadin jahar ta Taraba. Shitta ya kirayi bangarori masu zaman kansu da su shiga a dama dasu wajen bunkasa harkokin wasanni domin marawa gwamnatin baya wajen aniyrta na samarwa matasa aikinyi. Wasu daga cikin wadanda suka halarci horon wato Diana Sam-Aleng daga Makarantan sakandaren GDSs Gembu sai Lydia Simon daga makarantan Sakandaren GDSS Wukari East sun baiyana farin cinkinsu dangane da wannan horon da akayi musu tare da tabbatar da cewa zasuyi iya kakarinsu ganin cewa an horan da daluben irin wannan wasa tun daga matakin farko. Taron horon ya samu halartan ko odinatan kungiyar na jahar Akwa Ibom Grace Acaha dama sauransu .

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE