An baiyana cewa rikicin jam iyar A P C a jahar Taraba bazai hanata nasaraba a zabe maizuwa.Hassan Ardo.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Ko odinatan majalisar gangamin neman zaben dan takaran shugaban kasa a karkashi Jam iyar A P C Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a jahar Taraba Ambasada Hassan Jika Ardo yace duk da rkicin cikin gida da ya dabaibaye jam iua A P C a jahar Taraba Jam iyar zatayi nasara a Babban Zaben ahekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Ambasada Hassan Jika Ardo ya bayyana haka ne a lokacinda ya zantawa da manema labarai a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba.
Tsohon Jakadan yace kan yayan jam iyar a hade yake don haka nema yake tabbatar da cewa jam iyar zatayi nasara a zabe mai zuwa.
Ardo yace wasu makiyar jam iyar ne kawai ke kawo rudani a cikin jam iyar domin rarraba kan jam iyar wanda kuma baza su samu nasaraba domin kan jam iyar a jahar Taraba a hade yake asalima yan takaransu na jam iyar A P C zata samu naara a zaben majalisar dokoki ta kasa dana shugaban kasa wanda za ayi nan da makwanni.
Domin a cewarsa a tattauna da suka da al umma musammanma magoya bayan jam iyar dama na wasu jam iyun sun nuna cewa zasu zabi dan takaran shugaban kasa jam iyar wanda suke ganin zai kafa tarihi wajen gudana da shugabancinsa
Yace maganar gaskiya akwai wasu matsaloli musamanma dangane da dan takaran gwamna kuma da yardan Allah za magance matsalar don bazasu bari wasu su musu kutseba a cikin harkokin jam iya zasu cigaba da tattaunawa da jama a domin ganin anyi dukkanin abunda suka dace.
Don haka nema yace zaiyi amfani da wannan dama da ya kira dukkanin yan jam iyar A P C a jahar Taraba da akoda yaushe sukasance masu yin dukkanin abunda zaikawo cigaban jam iyar ta A P C.
Ardo ya kuma kirayi Al ummar jahar Taraba musammanma masu zabe da su fito kanau da kwarkwarkwatarsu domin zaben Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima azabe mai zuwa.
Comments
Post a Comment