An bukaci Babban Bankin Najeriya ya wadatar da sabbin kudade.

Masu sana ar fawa a jahar Adamawa sun koka dangane da karancin kudi da ake fuskanta biyo bayan canja fasalin kudin Najeriya wanda haka yayi sanadiyar koma bayan harkokin kasuwancinsu na fawa. Alhaji Babanna Palace ne yayi wannan kira a tattaunawarsa da jardar Al Nur a yola. Dangane da karancin kudi da ake samu. Babanna yace ya kamata gwamnatin ta duba yanayinda al umma ke ciki na matsalar rayuwa domin ta dauki matakin magance matsalar. Wanda acewarsa mutane sun shiga wani yanayi na matsin rayuwa. Babanna yace Babban matsalarma itace wasu masu shanun basu da asusun ajiya a banki bale a tura musu kudi don haka ne ya zama wajibi su kirayi gwamnati da ta dubi lamarin domin samawa al umma saukin rayuwa. Da wannan ne yake kira ga Babban Bankin Najeriya da ya wadata bankuna da sabbin kudaden domin ganin al umma sun samu saukin gudanar da harkokinsu yadda ya kamata ba tare da matsalaba. Ya kuma kirayi yan Najeriya da sukasance masu gudanar da adu o i a koda yaushe domin neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen rayuwa da al umma ke fuskanta. Ya kuma yi adu ar gani an kammala zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya .

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.