An kirayi Babban Bankin Najeriya da ya wadatar da sabbin kudadea bankunan kasuwanci.

An kirayai gwamnatin tarayya dama Babban Bankin Najeriya ta suyi dukkanin abunda suka dace domon wadatar da sbbin kudade a bankunan kasuwanci domin al umma su samu walwala biyo bayan kuncin rayuwa da suka shiga bayan canja fasalin kudaden Najeriya. Shugaban kunguyar masu sana ar P O S a jahar Adamawa Auwal Usman ne yayi wannan kira a zantawarsa da jarida Al Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Auwal yace karancin kudi a bankunan kasuwanci dama hanun jama a yayi sanadiya tabarbarewar lamura da dama ya kuma sanya mutane ciki wahalar rayuwa, saboda haka ya kamata Babban Bankin na Najeriya da gwamnatin tarayya su taimaka a samar da wadattun kudade domin ceto mutane daga halin da suke ciki a yanzu. Ya kuma shawarci masu manyan shaguna da masu gidajen mai da su mallaki na uran P O S domin shima zai taimaka wajen samun saukin matsalar. Ya kuma yi fatan ganin an kammala Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya ba tare da wata matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE