An samu gawar wani yaro da aka cire sassan jikinsa.

A safiyar lahdin nan ne aka wayi gari da ganin gawar wani yaro karami mai kimani shekaru sha biyu, wanda aka cirewa maqoshi da idanu da kuma harshe, sannan aka jefar dashi a wani lungu a unguwar Rumde dake bayan sakatariyar karamar hukumar Yola ta Arewa a Jihar Adamawa. Ana kyauta ta zaton Yaron Almajiri ne da har zuwa lokacin hada wannan Rahoton ba'a kai ga gano a wace makaranta yake karatu ba. Sai dai duk kokarin da akayi domin jin ta bakin mazauna unguwar da lamarin ya faru, Mutanen duk sunki cewa uffan kan lamarin Wani jami'in tsaro daga Jimeta Division ya tabbatar da cewa sun dauki gawar zuwa mutuware dake asibitin kwararru na specialist dake jimeta.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE