An shawarci matasa wajen zabe shugaba.

An kirayi matasa a fadin Najeriya da sukasance masu maida hankali wajen zaban shugaban da zai cire musu kitse a wuta ta wajen sama musu aikinyi domin dogaro da Kansu. Shugaban shuwagabanin matasan jam iyar P D P jahar Adamawa Hon. Abdulrahman Musa ne ya yi wannan kira a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola. Hon. Abdulrahman yace matasa sune suke da kaso mafi yawa na Al ummar Najeriya da ma kada kuri a saboda da haka bai kamata ace sunyi wasa da wannan dama da suke dashi wajen yin bangan siyasaba ya kamata sukasane jakadu na gari a tsakanin Al ummah. Musa ya kuma kirayi yan Najeriya Musammanma yan siyasa da cewa siyasafa abunda zai rarraba kai bane asalima siyasa yana kawo hadin kai dama cigaba harma da wanzar da zaman lafiya. Ya kara da cewa yakamata yan Najeriya su zabi jam iyar P D P a dukkanin matakai domin ceto kasan daga hali da take ciki a yanzu. A cewarsa dan takaran shugaban kasa a jam iyar P D P Alhaji Atiku Abubakar jajirceccenen a bangaren kasuwanci saboda haka in aka bashi dama zai bunkasa harkokin kasuwanci dama harkokin noma a fadin Najeriya baki daya. Don haka ne ma yake kira ga yan Najeriya da su baiwa wazirin Adamawa Alhaji Atiku kuri a domin cigaban al umman kasan nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE