An yabawa Al ummar jahar Adamawa bisa goyon baya da suka baiwa Hajiya Aishatu Binani.

An yabawa al ummar jahar Adamawa bisa hadin kai da goyon baya da suka baiwa yar takarar gwamna a Jam iyar A P C Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani a lokacinda ta gudanar da gangamin neman zabe a fadin jahar baki daya. Mallam Salihu Baba Ahmed ko odinatan gangamin yakin neman zaben sanata Aishatu Binani ne yayi wannan yabo a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola radar gwamnatin jahar Adamawa. Mallam Salihu Ahmed yace Al ummar jahar Adamawa sunyi abun a yaba saboda yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka nunawa Hajiya Aishatu Binani goyon baya don akwai fatan ganin zasu bata kuri a a ranan zabe. Alhaji Salihu ya kuma jinjinawa matasa a fadin jahar Adamawa ganin yadda aka gudanar da dukkanin yakin neman zabe ba tare da yin amfani da makamiba kuma basu nuna halayen na ta ammali da miyagun kwayoyiba saboda haka yana gode musu kuma dafatan zasuci gaba da nuna halaye na gari a koda yaushe domin samun cigaban domokiradiya a jahar dama kasa baki daya. Harwayau Salihu Baba Ahmed ya godewa Yar takaran gwamna a jam iyar A P C Hajiya Aishatu Binani dangane da yadda ta gudanar da neman zabenta batare da tayi kalamain batanci ga waniba ga kuma yadda take girmana masarautu gargajiya a duk lokacin da ta ziyarci fadar sarki. wannan ya nuna ana samun cigaban damokiradiya kenan. Don haka nema yake kira ga al ummar jahar Adamawa da su bata damar domin gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa baki daya. Ya kirayi daukacin Al umma jahar Adamawa da su cigaba da yin adu o i domin ganin an kammala Babban zaben shekara ta 2023 lafiya ba tare da matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE