Majalisar Addinin Musulunci a jahar Adamawa ta amice da Atiku Abubakar a matsayin dan takaran da zata zaba a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa ta amice da dan takaran shugaban kasa a jam iyar P D P Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda zasu zaba a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa. Shugaban majalisar addinin musulunci dake jahar Adamawa Aljahi Gombo Jika ne ya baiyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske jin kadan da kammala taron majalisar wanda aka gudanar a sakatariyar majalisar dake yola. Alhaji Gambo Jika yace majalisar tayi la akari da yanayin yan takaran inda suka cimma matsaya ganin cewa Alhaji Atiku zasu baiwa kuri arsu domin kasancewarsa dan jahar Adamawa ne wanda kuma suna da yakiinin cewa zai gudanar da aiyukan cigaban kasan nan. Alhaji Jika yace majalisar ta kuma yabawa hukumomin tsaro bisa na mijin kokari da sukeyi wajen daukan dukkanin matakai da sukeyi domin kare rayuka dama dukiyoyin Jama a. Ya kuma jinjinawa gwamnan jahar Adamawa bisa kokari da yakeyi na gudanar da aiyukan cigaban jahar dama inganta tsaro a fadin jahar baki daya. Wanda a cewarsa hakan ya taimaka wajen Samar da zaman lafiya. Harwayau majalisar ta yabawa hukumar zabe bisa kokari da takeyi tare da kara kira da tayi dukkanin abunda suka dace domin ganin an samu inganceccen zabe a Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Majalisar tace zatayi da wannan dama wajen kiran Al umma musulamai musammanma wadanda sukayi rijista zaben da su dtabbat sun mallaki katin zabensu domin shine zai basu damar zaban wanda suke so a ranan zabe. Dangane da majalisar dake shiyoyin kuwa sai Alhaji Gambo jika yace zasu yi nazarin ganin ko wayen za a zabe a matsayin majalisar dattawa dana wakilai a dukkanin shiyoyin dake fadin jahar ta Adamawa. An kuma gudanar da adu o i na misamman domin neman aimakon Allah Madaukakin sarki wajen ganin an gudanar da zabukan dake tafe lafiya ba tare da matsaloliba.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.