Rundunan yan sandan jahar ta Adamawa ta mika ta ziyarta ga iyalen marigayiya Maryam Abdullahi.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Afolabi Babatola a madadin rundunan yan sandan jahar Adamawa yana mai jajantawa iyalen marigaiya Maryam Abdullahi wanda ta gamu da ajalinta biyo bayan wani hatsaniya da ya faru a daren Alamis a kwalbatin Doubeli dake cikin karamar hukumar yola ta arewa.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa wanda kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya sanyawa hanu kuma aka rabawa manema labarai a yola.
Kwamishina yan sandan ya nuna rashin jindadinsa da aukuwar lamarin kuma yace rundunan tana da kyakkawar halaka da al ummar jahar Adamawa don haka nema rundunan ta gaggauta mika ta aziuarta ga iyale dama yan uwa marigayiyar tare da yi mata adu ar Allah ya jikanta da rahama.
Harwayau kwamishinan ya umurci mataimakin kwamishina mai kula da sashin binciken manyan laifuka wato CID da ya gaggauta bincike dangane da lamarin.
Bayan mutawar Maryam Abdullahi yan zu haka rundunan tana tsare da Aliyu Yusuf.
Comments
Post a Comment