An bukaci da al umma musulami su maiada hankali wajen tura yaransu makarantun addini dana zamani.

An kirayi iyaye da sukasance masu tura yaransu makarantu addinin musulunci domin ganin sun samu damar karatun All Qur ani mai girma domin ganin an samu wadattun makaranta Al Qur ani a tsakanin Al umma misulmai. Malam Aisha Adamu ce tayi wannan kira a lokacinda take yaye dalubenta wadanda suka sauke Al Qur ani mai girma a makarantarta da yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Malama Aisha tace karantar da yara karatun Al Qur ani mai girma tun suna yara yana da mutukan muhimmanci wanda acewarta hakan zai taimaka wajen samun matass mahaddata Al Qur ani da dama a tsakanin Al umma musulmai wanda hakan zai kawo cigaban addinin musulunci. Ta kuma kirayi matasa da suma su maida hankali wajen neman ilimin karatun Al Qur ani mai girma domin suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban addinin musulunci yadda ya kamata. Harwayau ta kirayi wadanda suka sauke da suyi amfani da karatun nasu domin ciyar da addinin musulunci gaba da kuma wanzar da zaman lafiya a jahar dama kasa baki daya. Itama anata jawabi Batista Fatima Raji race tazone domin ta shaida bikin saukan kuma ta ji dadin tare da farin cikin ganin yadda taga kananan yarane suka samu damar sauke al Qur ani. Itama shawartansu tayi da sukasnce masu amfani da abinda aka koya musu domin bunkasa ilimin addinin musulunci yadda yakamata. Wasu daga cikin wadanda suka sauken sun baiyana farin cikinsu tare da godiyarsu ga malamrasu wato mlama Aisha bisa jajircewa da tayi wajen karantar da su tare dyi al kawarin yin amfanin da abinda suka koya domin samun cigaban addinin musulunci. Sama da yara ashirin da hudu ne dai suka sauke all Qur ani a wannan shekara ta dubu biyi da ashirin da uku.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.