Anja hankalin matasa da suyi dukkanin abunda zai kawo cigaban kasa.

An shawarci matasa dake fadin jahar Adamawa da su kasance masu hada Kansu da kuma yin dukkanin abinda suka dace domin samun cigaban rayuwarsu su kuma kasance masu shiga adama dasu a cikin harkokin siyasa domin suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban jahar dama kasa baki daya. Sarkin matasan Adamawa kuma wanda yayi nasaran lashe zaben kujeran majalisar wakilain tarayyar Najeriya a mazabar Kananan hukumomin Fufore da Song a jahar Adamawa Alhaji Aliyu Wakili Boya ne ya bada wannan shawara a lokacin da ya marabcin tawagan matasa da suka kai mass ziyaran murnan nasara da yayi a zaben da aka gudanar a asabar din da ta gabata. Alhaji Aliyu Wakili yace matasa sune shuwagabanin gobe saboda haka ya kamata sukasance masu yin karatun ta nisu da kuma hangen nesa wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata. Wakili Boya wanda yayi samun nasaran lashe zabe a karkashin jam iyar A P C ya nuna godiyarsa ga daukacin Al ummar jahar Adamawa musamanma mazabarsa bisa wannan karamci da suka nuna masa wanda kuma hakan ya bashi damar zama dan majalisar wakilain tarayyar Najeriya don haka ya zama wajibi ya godewa al umma. Ya kuma kirayi al umma da su bashi hadin kai da goyon baya domin ganin ya cimma burinsa na gudanar da aiyukan cigaban maabarsa. Tare da yin Adu ar Allah madaukakin sarki yasa kar yaji kunya wajen gudanar da aiyukan cigaban mazabarsa. Har wayau Wakili Boya yace a shirye yake wajen karban shawarwari akan dukkanin abinda zai kawo cigaba a mazabarsa dama jahar baki daya. Ya sake jaddada farin cikinsa dangane da nasaran ya samu tare da kiran Al umma misammanma matasa da su kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma musammanma yadda aka tikari zaben gwamna da na majalsun dokokin jihohi. Ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da su cigaba da yin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a jaha dama kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE