Sanatan mazabar Arewacin jahar Taraba ya sake lashe zabe karo na biyu.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Sanata mai wakiltan Mazabar Taraba ta arewa a majalisar dattawar Najeriya Sanata Shu aibu Isa Lau ya sake lashe kujeran sanata a yankin karo na biyu.
Sanata Isa Lau wanda a yanzu haka shine mataimakin shugaban marassa rinjaye a majalisar dattawan Najeriya. Wanda kuma yayi nasara a zaben da aka gudanar a ranan asabar din da ta gabata.
Yankin mazabar arewacin jahar Taraba dai sun hada kananan hukumomin Jalingo, Lau, Karim Lamido, Zing, Yaro, da kuma Ardo Kola.
Da yake aiyana sakamokon zaben wanda ya baiwa sanata nasara mataimakin shugaban Jami ar tarayya dake Wukari Farfesa Chibiya Paul Chingu yace sanatan ya samu nasarane da kuri u dubu saba in da hudu da Dari shida da arba in da biyar inda abokin hamaiyyarsa Sani Abubakar Danladi yazo na biyu da kuri u dubu sittin da daya da dari takwas da saba in da takwas.
Sanata Sani Abubak ar Danladi ya dai tsaya takaran sanata ne a karkashin jam iyar A P C a yayinda Shikuwa sanata Shuaibu I sa Lau ya lashe zaben ne karkashin jam iyar P D P.
A jawabinsa kwamishinan hukumar zaben a jahar Taraba Umar Muktar Gajiram yace an gudanar da zabe mai inganci a fadin jahar ta Taraba.
Umar Muktar Gajiram ya baiyana haka ne wa manema labarai jin kadan da kammala sanar da sakamokon zaben shugaban kasa dana majalisun dokokin taraya a shelkwatan hukumar dake Jalingo. Ya kuma tabbatar da cewa hukumar zata magance kalubae da suka fuskanta a zaben gwamana da na majalisun dokokin jihohi wanda za ayi nan gaba kadan a fadin jahar.
Comments
Post a Comment