Wakili Boyi ya godewa mazabarsa bisa zabansa da sukayi.
Alhaji Aliyu wakili Boya sarkin matasan Adamawa kuma wanda yayi nasaran cin zaben dan majalisar wakilain tarayyar Najeriya na mazabar Fufore da Song a jahar Adamawa, yana mai mika godiyarsa ga daukacin Al ummar jahar Adamawa musammanma mazabarsa bisa zabarsa da sukayi na dan majalisar wakilai tarayya,
Alh. Wakili Boya yana mai farin ckin bashi dama da mazabarsa sukayi kuma da yardan Allah bazai basu kunyaba domin acewarsa zai dukkanin iya kakarinsa na kawo aiyukan cigaban mazabarsa.
Don haka nema yake kara kira ga al ummar mazabarsa da sukasance masu yin adu o i wanzar da zaman lafiya a yankin da jaha dama kasa baki daya.
Ya kuma bukacin al ummar su bashi hadin kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan mazabarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da samun matsaloliba.
Ya kuma shawarci matasa da sukasance masu bada tasu gudumawa wajen cigaban jahar dama kasa baki daya.
Comments
Post a Comment