Za Kuga Chanji Cikin Kwanaki Dari na farko A Ofis- Zababben Gwamnan Taraba, Agbu

Daga Sani yarima Jalingo. Za Kuga Chanji Cikin Kwanaki Dari na farko A Ofis- Zababben Gwamnan Taraba, Agbu Zababben Gwamnan Jihar Taraba, Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) yace da yardan Allah zasu kawo chanji na zahiri cikin kwanaki dari na farko da za suyi a ofis. Agbu ya sanar da hakan ne a lokacin da yake yiwa dunbin magoya bayan Jam'iyyar su ta PDP yawabin godiya jim kadan bayan ya karfi takardan shedan zaben sa daga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC dake Jalingo. Kwamishinan zabe na hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC dake Jihar Taraba, Umar Muktar Gajiram shine ya mikawa zababben Gwamnan Jihar, Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) takardan shedan zaben sa a ranar laraba 29 ga watan maris na 2023 da muke ciki. Hakanan kuma, Umar Muktar Gajiram ya mikawa suma zababbun 'Yan Majalisan dokokin jihar ta Taraba guda 24 takardan shedan zaben su a dakin da aka gudanar da tattara sakamakon zaben Gwamnan Jihar wanda ya gudana a ranar 18 ga watan maris din dake cikin haraban hukumar zaben a garin Jalingo. Da yake yiwa dunbin magoya bayan sa da Jam'iyyar su ta PDP yawabin godiya, zababben Gwamnan Jihar, Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) yace da yardan Allah zasu tafiyar da gwamnati ne na kowa da kowa domin hada kan al'umma, samar da zaman lafiyalafiya. "Batun addini wannan tsakanin Mutum ne da Allah, saboda haka Ina rokon ku ku taya mu da addu'a, dawan sukayi da wanda ma ba suyi ba dukkan mu daya ne, zamu sami zaman lafiya a Taraba, zamu hada kai, duk abinda gwamnati ya kamata tayi za muyi shi da yardan Allah," inji Kanal Agbu. Ga wasu daga cikin jama'an da suka dalarci taron inda suka Yi fatan alheri da rokon iri daga sabuwar Gwamnatin mai zuwa. Sun roki Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) daya duba wadan da suka yi ritaya daga aikin gwamnatin jihar kuma ba'a biyasu hakkin su ba na tsawon shekaru. Mr. Nelson Len, Uwargida Veronica Alhassan, Gimbiya Batulu Muhammed, Mr. Gideon Katabs, Alh. Musa Abdullahi Chul, da Tsohon Kakakin Majalisar dokokin jihar Taraban, Peter Abel Diah na daga cikin zababbun 'Yan Majalisan dokokin jihar guda ashirin da hudu. Gimbiya Batulu Muhammed daga Gashaka, da Veronica Alhassan daga Bali ta daya zasu kasance mata guda biyu cikin 'yan Majalisar dokokin jihar kashi na goma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE