Akalla marayu dubu daya da dari biyar ne suka samu tallafin..

Kungiyar Jama atu Nasril Islam bangaren mata ta taimakawa marayu da kayaking sallah da abincin domin Suma su samu saukin gudanar da bikin sallah cikin tsanaki. Da take jawabin a wurin rarraba kayakin mataimakiyar Amiran kungiyar ta JNI a jahar Adamawa Hajiya Halima Muktar ta kurayi Al umma musulmai musammanma wadanda ke kula da marayu da su Kara maida hankali wajen kula da marayu tare da turasu makarantun addinin dana zamani domin su samu inganceccen ilimi a tsakanin Al ummah. Halima ta Kuma shawarci masu kula da marayu da daure kada sukasance masu tura talla suna gararamba a kan titi Wanda Kuma haka bazai amfanesuba. Ta Kuma kurayi iyaye da sukasance masu yiwa yaransu adu o I a Koda yaushe domin ganin sun kasance yara na gari a tsakanin Jama a. Itama anata jawabin sakatariya kungiyar ta JNI bangaren mata Hajiya Fatimatu Shuaibu ta baiyana dalilimsu na tallafawa marayu Wanda acewarta sunga ya dace marayum Suma sukasance tamkar wadanda suke da mahaifi a duniya su samu suyi walwala kamar kowa a lokacin bikin sallah. Don haka nema take kira ga wadanda suka samu tallafin da suyi amfanin da abinda suka samu ta hanyar da ta dace domin samun saukin rayuwa. Wasu daga cikin marayu da suka samu taimakon sun baiyana farin cikinsu da Jin dadinsu dangane da wannan taimakon da kungiyar ta JNI tayi musu tare da yin fatan Alheri ga kungiyar ta JNI bangaren mata. Cikin kayakin da aka taimakawa marayu dai sun hada da shinkafa, Mai,maggi, turamain zani ,yaduna da dai sauransu. Marayu dubu daya da dari biya wadanda aka zakulo daha gidaje dari da hamsin ne dai suka amfana da tallafin kayakin abinci dama kayan sawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE