An baiyana matasa dacewa suna gudumawa da zasu iya bayarwa a tsakanin al umma Sheik Duguri.
An kirayi matasa da sukasance jakadu na gari a tsakanin Al umma domin sune kashin bayan kowace Al umma a fadin duniya.
Sheik Ibrahim Muhammed Dugri wakilin malamai Bauchi Kuma shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala Mai shelkwata a Jos shiyar Abuja ne yayi wannan kira a ganawarsa da manem labarai a yola.
Sheik Ibrahim Muhammed yace matasa suna da rawa da zasu iya takawa wajen gudanar da aiyukan cigaban Al umma don haka ya Kamata Suma su bada tasu gudumawar wajen cigaba dama wanzar da zaman lafiya.
Malamin addinin musulunci ya Kuma shawarci matasan da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Al umma Mai makon hakama kamatayayi suyi dukkanin abinda zai hada kan Jama a dama cigaban zaman lafiya yadda ya Kamata.
Ya Kuma kirayi matasa da su kaucewa yin bangan siyasa sukasance masu hada kansu da girmama shuwagabanin tare dayiwa iyaye biyayya Wanda acewarta Hakan zaisa su samu Albarka a rayuwarsu a Koda yaushe.
Malamin ya Kuma baiyana cewa iyaye mata Suma suna da muhimmiuar rawa da zasu iya takawa wajen baiwa yara tarbiya. Don haka Yana da mutukan muhimmanci iyaye mata su maida hankali wajen tarbiyar yara yadda ya Kamata.
Harwayau ya kirayi daukacin Al umman Najeriya da sukasance masu hada kansu da Kuma yin adu o I a Koda yaushe domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya Baki daya .
Comments
Post a Comment