An bukaci gwamnatin tarayya dana jahar su inganta tafkin geriyo Abdulrazak.
An kirayi gwamnatin tarayya dana jiha da suyi dukkanin Mai yiwa domin yashe tare da inganta tafkin geriyo domin samun cigaban dama bunkasa tattalin arzikin jahar dama kasa Baki Daya.
Sarkin ruwan tafkin na geriyo Alhaji Abdulrazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a lokacin da aka nude tafkin domin kama kifi da akeyi shekara shekara a tafkin dake cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Abdulrazak Abubakar yace kama kifi da akeyi Yana taimakawa sosai harma da Samar da sana o in dogaro da Kai ga matasa. Baya ga kamin kifin ana noma abubuwa da dama a baking tafkin na geriyo Wanda Kuma hakan yana kawo cigaban da dama a bangarori daban daban.
Da wannan ne yaga ya Kamata su kirayi gwamnatin da masu ruwa da tsaki da su taimaka domin kaiwa tafkin dauk duba da irin matsaloli da suke fuskanga wani lokacima ruwa tafkin kafewa yakeyi.wanda Hakan yana janyo asara masu yawa.
Da yake magane dangane da kama kifin kuwa sai Abdulrazak yace bana an samu kifi duba da yawa Jama a da aka samune yasa kifin ke wahalar samuwa.
Yace kawo yanzu dai masarautar Adamawa ne ke kula da tafkin Wanda Kuma masarautarnema ke bada izinin bude ruwan domin kama kifin. Kuma kawo yanzu ana samu cigaba sosai a bagarori daban daban na harkokin da ake gudanarwa a tafkin dama kewayen tafkin.
Comments
Post a Comment