An ja hankalin iyaye mata wajen baiwa yaransu tarbiya.
Domin ganin an samu cigaban tarbiyatatar da yara an kirayu iyaye musammanma mata da sukara himma wajen baiwa yaransu tarbiya domin samun cigaban matasa a tsakanin Al umma.
Mataimakiyar Amiran Kungiyar Jams atu Nasaril Islam bangaren mata Hajiya Halima Muktar ce ta bada wannan shawara a lokacin da take jawabi a wurin biking rufe tafsirin karatun Al qur ani mai girma WandaSayyida Hindu Dahiru Bauchi ta gabatar a yola.
Hajiya Halima race sun dauki kwararan matakai daban daban na ganin cewa sun fadakar da mata abubuwa da yawa ta yadda zasu kula da tarbiyar yaransu dama sana o in dogaro da kai wanda acewarta daukan matakin haka zai taimaka wajen karawa matan kwarin gwiwar yiwa yaransu tarbiya.
Hajiya Halima ta kara da vewa bays ga tafsirin da aka gabatar an gudanar da lacoci daban daban da zummar wayarwa matan kai dangane da yadda zasu tarbiyatar da yaransu da kuma koyon sana ar dogaro da kai..
Ta kuma kirayi al umma musulmai da su rubaiyya ibadarsu a kwanaki goma na karshen watan Ramadan da kuma adu o i domin nemana taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki daya.
Da take gabatar da nasiha Hajiya Fatima Ahmed Farafa ta ja hankalin all umma musulmai da sukasance masu tsaron Allah madaukakin sarki a koda yaushe domin samun tsira ranan gobe kiyama.
Hajiya Fatima ta kuma kirayi mata musammanma wadanda suka saurari tafsirin All qur ani mai girma da suyi amfani da darusa da sukaji a wurin tafsirin wanda acewarta hakan zai taimaka wajen wanzar da zamam lafiya a tsakanin al umma baki daya.
Shima a jawabinsa shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika godiya yayiwa wadanda suka shirts wannan tafsirin tare da shawartansu da sucigaba da gudanar da aiyukan addinin musulunci domin cigaban addinin musulunci yadda ya kamata.
Ya kuma ja hankalin al umma musulmai wajen hada kai a tsakanin al umma musulmai domin acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban zaman lafiya a tsakanin jama a yadda yakamata.
SP Ahmed Suleiman Babban limamin Masalacin Jumma a na barikin yan sanda a jahar Adamawa shima jaddada kiransa yayiwa al umma musulmai da sukasance masu Santa tsaron Allah a zukatansu a koda yaushe domin samun tsira ranan gobe kiyama.
Malam umar Bappari kem shima shwartan matan yayi da suyi amfanin da abunda sukaji a wurin tafsirin da ma fadakar da wasu wadanda basu samu damar zuwaba.
Comments
Post a Comment