An sahawarci yan jahar Adamawa sukasanve masu hada kansu. Gwalan
An shawarci Al ummar jahar Adamawa musammanma wauraren da za a sake zabe a wasu mazabu da ke fadin jahar Adamawa. da su kasance sun fito sunyi zabe cikin tsanaki ba tare da matsaloliba domin Samar da zakan lafiya da ma cigaban jahar ta Adamawa baki daya.
Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya bada wannan shawarci a lokacin da ya zanta da jaridar Al Nur a yola. Fadar gwamnatim jahar Adamawa.
Alhaji Muhammed Saleh yace yakamata Al ummar jahar Adamawa su sani bamu da wata jahar da ta wuce jahar Adamawa don haka akwai bukatar a hada Kai domin a gudanar da zaben lafiya.
Alhaji Gwalan ya ja hankalin Al umma da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali da Kuma kada mu bari Yan siyasa suyi amfanin da mu wajen yin abinda Bai daceba a lokaci dama bayan zabe.
Ya Kuma shawarci matasa da Suma su bada tasu gudumawa wajen gina kasa dama gina dumukiradiyya kasancewa sune kashin bayan Al umma don haka kar su bari ayi amfani da su wajen ta-da fitina a lokaci dama bayan zabe.
Har wayau ya kiray daukacin Al umma musulmai dasuyi afmani da wannan lokaci na azumi domin yin adu o I wanzar da zaman lafiya a fadin jahar da ma kasa baki daya.
Comments
Post a Comment