An taya Babbar Alkalain jahar Adamawa murna rundunan yan sandan jahar Adamawa.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taya Hon. Hapsat Abdulrahman murnan kasancewarta Babban Alkalain jahar Adamawa.
Rundunan ta baiyana hakane a sakon taya murna dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje.
A sakon murnan anjiyo Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yanaceawa nada Hon. Hapsat Abdulrahman a matsayin Babban Alkalain jahar Adamawa ta cancanta kasancewarta mace ta farko da zama Babbar Alkalain a jahar Adamawa.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa ya kuma tabbatar da cewa rundunan a shirye take tayi aiki kafada da kafada domin ganin an samu nasaran yakan ta addamci a fadin jahar baki daya.
Don haka kwamishinan yace a madadinsa da sauran Jami an rundunan na taya maishari a Hapsat Abdulrahman murnan samun wannan mukami na Babbar Alkalin Alkalain jahar Adamawa.
A ranan talatan nan ne dai gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya tabatarwa maishari a Hapsat Abdulrahman Babbar Alkalain jahar Adamawa bayan da aka Bata rikon kwaryan mukamin.
Comments
Post a Comment