Anja hankalin Al umma musulmai wajen yin ibada a kwanaki goma na karshen Ramadan.

An shawarci Al umma musulmai da suyi amfanin da wannan lokaci na kwanaki goma na karshen wata azumim Ramadan wajen rubayya ibada da adu o I domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Nakeriya Baki Daya. Shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne yayi wannan kira a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola. Alhaji Gambo Jika yace kwanaki goma na karshen watan Ramadan suna da mutukan muhimmanci ga Al umma musulmai don haka Bai Kamata ace musulmai sunyi sakaciba wajen yin adu o I da ibada. Wanda acewarsa Hakan zaitaimaka wajen samun saukin tayuwa ga Al umma Baki Daya. Alhaji Gambo ya Kuma kurayi malamai musammanma masu gudanar da tafsirin azumi da su maida hankali wajen yin was azin dukkanin abinda zai kawo hadin Kai a tsakanin Al ummah musulmai dama sauran Al umma Baki Daya. Ya Kuma shawarci Al umma musulmai da sukasance masu tausayawa juna dama taimakawa juna a Koda yaushe domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata. Suma iyaye an shawarcesu da suyi amfanin da wannan lokaci wajen yiwa yaransu adu o I domin ganin sun samu tarbiya dama shiriyar da ta dace a tsakanin Al umma

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.