Gidauniyar Attarahum ta taimaka da kayakin Azumi a jahar Adamawa.
Gidauniyar Attarahum ta taimakawa marassa galihu da kayakin Azumi domin su samu saukin rayuwa atsakanin al umma a wannan lokaci na azumin watan Ramadan.
Gidauniyar tayi wannan taimakonne a yola ga wadanda suka fito daga sassa daban daban daga ciki da wajen fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Da yake jawabi a lokacin rabon kayan shugaban Gidauniyar ta Attarahum a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib yace sun dauki matakin wannan taimakonne duba da yanayi da yanayi da ake ciki na azumi domin neman yardan Allah madaukakin sarki tare da samun lada mai yawa.
Mallam Muktar yace ankafa gidauniyar Attarum ne domin taimakon kai da kai don haka nema suka ga ya dace su fadada taimakon zuwa ga al ummah daban daban.
Mallam Muktar ya kuma kirayi kungiyoyi dama masu hanu da shuni sukasance masu taimakawa marassa galihu a koda yaushe domin samun cigaba yadda ya kamata.
Ya kuma jaddada aniyar gidauniyar na cigaba da taimakawa al umma a koda yaushe domin ganin al umma sun samu saukin rayuwa yadda ya kamata.
Shima a jawabinsa sakataren gidauniyar a jahar Adamawa Mallam Mamman Nasir ya kirayi wadanda suka samu taimakon da suyi amfani da suka samu ta hanyar da ya dace domin ganin abinda suka samu ya amfaƱesu yadda ya kamata.
Ya kuma kirayi al ummah musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na azumi wajen yin Adu o i samar da zaman lafiya a fadin kasan nan baki daya.
Wasu daga ciki wadanda suka samu taimakon sun baiyana farin cikinsu dangane da kayakin da aka taimaka musa tare da godewa gidauniyar ta Attarahum bisa irin wannan taimako da akayi musu, wanda acewarsu gidauniyar Attarahum ta taimaka musu a dai dai lokacin da ya kamata tare da yin adu ar Allah ya daukaka gidauniyar.
Cikin kayakin da aka rarraban sun hada da shinkafa, suga, Taliya da dai sauransu.
Bikin bada taimakon dai ya samu halartan daukacin shuwagabannin gidauniyar ta Attarahum dake jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment