Hukumar NAFDAC a Najeriya tasha alwashin daukan matakin daina amfani da sanadiren dake canja launin fata a fadin Najeriya.

Hukumar inganta abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC tace nan gaba kadan zata fara tilastawa na daina yi da Kuma sayar da sanadaren dake canja launin fata a fadin kasan nan baki daya Babban darektan hukumar ta kasa farfesa Mojisola Adeyeye ce ta baiyana haka a wurin taron karawa juna sani Wanda hukumar ta shiyawa yan jarida a yankin arewa masaugabas dangane da hatsarin yin amfani da sanadaren dake sauya launin fata. a Maiduguri fadar gwamnatin jahar Borno. Babbar darektar Wanda darektan sashin sanadaren hukumar Dr Leonard Omokpariola ya wakilta tace an shiyar irin wannataro wa yan jarida a jihohin Kano, Enugu, Lagos, Abuja, Jos, Ibadan, da Kuma Port Harcourt. Tace hukumar ta lura cewa yin amfani da sanadaren dake canja launin fata yana barazana da lafiyar lamarin akalla mata a Najeriya Kaso Saba in da bakwai suna amfani da sanadaren . Farfesar tace hakan yasa suka nemi hadin kana yan jarida domin su wayarwa Al umma Kai dangane da illar da yin amfani da sanadaren dake canja launin fata kedashi. Ta Kuma baiyana cewa shirya irin wannan taro da ga cikin irin kokari da hukumar keyi na kawarda amfani da duk wani sanadarin da ake amfani dashi wajen canja launin fata Wanda Kuma yan jarida suna da rawa da zasu iya takawa wajen wayarwa Jama a Kai dangane matsalar Baki daya. Shima anashi jawabi darektan hukumar ta NAFDAC a yankin arewa masau gabas Dr Bukar Usman yace dangane da matsalar da canja launin fata hukumar zata wayarwa manoma Kai dama masu sayarda kayakin marmari a fadin yankin Baki Daya. Darektan yada labarai hukumar Dr Abubakar Jimo yace kawo yanzu hukumar da horas yan jarida dari takwas dangane illar amfani da sanadaren dake canja launin fata a fadin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE