Kungiyar manoman auduga a jahar Adamawa ta taya gwamna Fintiri murnan cin zabe.
Kungiyar manoman auduga a Najeriya shiuar jahar Adamawa tana Mai Yaya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cin zabe a matsayin gwamna jahar Adamawa a zaben gwamna da aka gudanar a wannan shekara ta 2023.
Shugaban kungiyar a jahar Adamawa Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola.
Alhaji Muhammed Saleh yace a madadin kungiyar da membobinta suna taya gwamna murnan lashes zaben da shi da mataimakiyarsa Farauta.
Sanarwa ta Kuma kirayi Al ummar jahar ta Adamawa ta su baiwa gwamnan hadin Kai da goyin baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar Baki Daya.
Harwayau sanarwa ta taya gwamnan murnan bikin karamar sallah da fatan Allah ya karbi ibada ya Kuma maimaita mana Amin.
Alhaji Saleh ya Kuma kirayi daukacin Al umma jahar Adamawa da su cigaba da yiwa jahar dama kasa adu o I samar da zaman lafiya.
Comments
Post a Comment