Kungiyar yan jarida a jahar Adamawa ta taya gwamna Ahmadu fintiri murnan lashe zabe.
Kungiyar yan jarida a Najeriya shiyar jahar Adamawa tana mai taya gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri murnan samun nasaran lashe zaben gwamna da akayi ran sha takwas ga watan hudu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Kungiyar ta NUJ shiyar jahar Adamawa ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun shugaban kungiyar a jahar Adamawa Ishaka Donald Dedan tare da sakataren kungiyar Fidelis Jocktan.
Sanarwan tace a madadin dukkanin membobin kungiyar dama shugabancin kungiyar suna masu farincinkin taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murna yin nasaran cin zaben gwamna da aka kammala a jahar Adamawa.
Na saran da Fintiri yayi ya biyo nayan irin aiyukan cigaban jahar musammanma a yankunan karkara da ma gudanar da shirye shiryen koyar da sana o i dagaro da kai da dai sauransu.
Nasarawan ta kuma yaba da yadda al ummar jahar Adamawa sukuma kasance masu hakuri a koda yaushe domin samun cigaban jahar ta Adamawa baki daya.
Kungiyar tana mai adu ar sabon zabebnen gwamnan zaicigaba da aiyukan cigaban jahar tare da hada hanu da yan adawa domin cimma nasaran a fadin jahar baki daya.
Kungiyar ta kuma yabawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC dama al umma jahar Adamawa bisa yadda aka gudanar da zaben gwamna a ranan shatakwas ga watan hudu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Comments
Post a Comment