Munataya gwamana fintiri murnan cin zabe NULGE
Kungiyar ma aikatan kananan hukumomi a Najeriya NULGE shiyar jahar Adamawa tana taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cin zaben gwamna jahar Adamawa.
Shugaban kungiyar ta NULGE a jahar Adamawa Hammajumba Gatugal ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola.
Hammajumba yace a madadinsa dama membobin kungiyar dake jahar Adamawa suna masu farin cikin taya gwamnan dama mataimakiyarsa murnan nasaran lashe zabe da sukayi bayan kammala zaben gwamna da aka gudanar.
Ya Kuma sahawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu hada kansu da Kuma baiwa gwamnan hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.
Comments
Post a Comment