Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta cafke mutene biyu da aka zargi dayin garkiwa da mutane.

Rudunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cafke mutane biyu da ake zargi masu garkiwa da mutane ne a cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Kakakin rudunan yan sandan na jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace rudunan ta samu nasaran kama mutane biyu da ake zargi ne biyo bayan bayanain sirri da aka samu dangane da wadanda ake zargi. Wanda Kuma hakan yada rundunan natayi da wasaba inda ta Kai samamai tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane dake cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Rundunan ta dauki matakin hakane biyo bayan rahoton da suka samu na yin garkuwa da Aisha Ahmadu da maigidanta Ahmadu Muhammed tare da kashe Mai gidannata a kauyen Digil dake ciki karamar hukumar Mubi ta arewa. Wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa da yakai nera Milyon biyu da dubu dari biyar kafin su Sako mutane. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya yabawa D P O karamar hukumar Mubi ta arewa bisa kokarinsu na kama tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane. Kwamishinan ya Kuma tabatarwa gwamnatin jahar Adamawa dama Al umma dake fadin jahar cewa rundunan ta kimtsa tsaf domin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma dake fadin jahar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE