Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta kama mutane tara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

A kokarinta na kawar da aikata taddajci a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kamar mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa biyo bayan farmaki da ta gudanar a sassa daban daban dake fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace an samu nasaran kama wadanda ake zargi ne biyo bayan baiyanai sirri da suka samu Wanda hakan yasa kwamishinan Yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola baiyi da wasaba inda ya tura Jami an tsaro domin kamosu daga maboyansu. Rundunan karkashin jagorancin kwamandan CRACK tare da hadin gwiwar mafarauta ne dai suka kai samamen tare da nasaran cika hanu da wadanda ake zargi. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsu da jin dadinsa dangane da na mijin kokari da Jami an tsaro sukayi wajen kama mutane ya kuma kirayesu da su Kara himma domin ganin an magance matsalar aikata laifuka a fadin jahar baki daya. Rundunan yan sandan ta Kuma gano makamai da suka hada da binga Kiran Ak 47 guda hudu dama wasu makamai a wurin wadanda ake zargi Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa ya kuma tabbatar da cewa da zaran an kammala bincike akansu za a gurfanar da su gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.