Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da inganta tsaro a lokacin bikin karamar Sallah.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta ce ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin inganta tsaro a lokaci dama bayan bukukuwar karamara Sallah.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahay Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola.
Sanawarn na cewa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya tabbatarwa al umma jahar Adamawa cewa rundunan ta dauki kwararar matakan tsaro domin ganin an kare rayuka dama dukiyoyin al umma a lokacin bukukuwar karamar Sallah don haka al umma su gudanar da aiyukansa bisa doka su kuma kaucewa abinda zaiyiwa doka karan tsaye a lokacin bukukuwar Sallah.
Kwamishinan ya kuma umurci mataimakinsa dake da aiyukan rundunan da ya tabbatar cewa angudanar da bukukuwar Sallah lafiya ba tare da matsaloliba a dukkanim yankuna dake fadin jahar ta Adamawa.
Rundunan ta kuma taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Murnan dama al ummar jahar Adamawa murnan bikin karamar Sallah a wannan shekara.
Kwamishinan ya kuma kirayi al ummar jahar ta Adamawa da su gudanar da bikin Sallah cikin tsanaki tare da bin doka da oda da kuma kai rahoton dukkanin abinda basu amince dashiba.ta kira wadannan numbobin wayar kamar haka
08089671313
08032718516
08031153243
Comments
Post a Comment