Wani dan shekaru saba in da haifuwa. ya shiga komar yan sanda bisa zarginsa da yin fyade a jahar Adamawa.

Rundunan yan sandan jajar Adamawa ta cika hanu da wani mutum dan shekaru saba in da haifuwa bisa zargginsa da yiwa wasu kananan yara biyu fyade a jahar ta Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace mutumin mai suna Usman Ibrahim ya shiga koman yan sandan ne biyo bayan rahoton da uban yaran ya kai ofishin yan sandan dake Jimeta a cikin karamar hukumar yola ta arewa. Wanda hakan yasa Jami an yan sandan basuyi da wasaba wajen damko wanda ake zargin. Sanarwan ta cigaba da cewa ana zargin mutuminne da yaudaran yaran zuwa daki a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa karatun saboda haka sai yayi amfani da wannan damar. Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiwa sahin binciken manyan laifuka wato CID damar gudanar da bincike kan lamarin. A binciken farko da aka gudanar dai an gano cewa mutumin yana yara uku kuma yanzu haka yana zaune ne ba tare da mataba har tsawon shekaru goma. Yaran da ake zargi ya musu fyaden dai shekarunsu ya kama daga hudu zuwa bakwai. Kuma da zaran an kammala bimcike akansa za a gurfanar dashi gaban kotu domin ya fuskanci shariya. Kwamishinan yan sandan ya kirayi al ummar jahar ta Adamawa da sukasance masu taimakawa yan sandan da duk wasu bayanai da zai taimaka wajen kama irin wadannan batagari a tsakanin al ummah. Ya kuma batarwa al ummar jahar Adamawa musammanma iyaye cewa rundunan yan sandan a shirye take wajen yin yaki da cin zarafin yara da kuma tura keyar duk wanda aka samu da cin zarafin yara zuwa kotu. Shidai Usman Ibrahim mazauni ne a Ajiya Street dake cikin garin jimeta a karamar hukumar yola ta arewa kuma bai da nesa da gidan yaran da ake zargi da yi musu fyade,

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE