An kirayi gwamnatocin jihohi dana kananan hukumomi da su maida hankali wajen tallafawa manoma . Manu Ngurore.

An kirayi gwamnatin jihohi dana kananan hukumomi da su maida hankali wajen taimakawa manoma a koda yaushe domin samun cigaban harkokin noma dama bunkasa tattalin arziki baki daya. Alhaji Usman Abubakar wanda kuma shine sakataren kungiyar manoma auduga a jahar Adamawa ne yabaiyana haka azatawarsa da manema labara a yola. Alhaji Usman yace kawoyanzu gwamnatin tarayyace kawai da ke taimakawa manoma wanda kuma hakan yasa manoman ke fuskatar kalu bale da dama, don haka akwai bukatar gwamnatin jihohi dana kananan hukumomi suma sukasance suna tallafawa manoman domin ganin an samu wadaceccen abinci a fadin Najeriya baki daya. Alhaji Abubakar ya kara kira da cewa gwamnatocin sukasance suna taimakawa manoman da kayakin noman akan lokaci wanda hakan zai baiwa manoman damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata. Ya kuma shawarci gwamnatocin da su maida hankali wajen shiryawa manoma taron bita musammanma wadanda ke yankunan karkara domin fadakar dasu yadda ake guadanar da harkokin noma a zamunance duba da yadda a yanzu harkokin noma ya koma na zamani. Haka kuma ya kirayi shuwagabanin manoma da suma su taka tasu rawan wajen taimakawa manoman ta bangaren samar musu da inganceccen iri da dai sauransu. Ya kuma bukaci gwamnati da kara himma wajen tura malamain gona zuwa yankunan karkara domin wayarwa manoman kai dangane da yadda zasu gudanar da harkokin nomansu ba tare da wasu matsaloliba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE