Kungiyar Sullunawa a jahar Adamawa ta kudiri aniyar kawo kashen rikici a tsakanin manoma da makiyaya.
A yayinda damina ke karatowa ne da an kirayi manoma da makiyaya da sukasance masu fahintar juna da hada kansu a koda yaushe domin samun zaman lafiya a tsakaninsu da ma cigaban aiyukansu yadda ya kamata ba tare da matsalaba.
Shugaba kungiyar Sullubawa ta kasa NASAN shiyar jahar Adamawa Alhaji Bello Ardo ne yayi wannan kira a lokacinda yake zantawa da manema labarai a Yola.
Alhaji Bello Ardo yace ya zama wajibi suja hankalin manoma da makiyaya duba da yadda aka fuskaci damina wanda kuma alokaci daminane akafi samun rikici a tsakanin manoma da makiyaya. Don hakane ya kamata akirayi manoma da makiyayan da sukasance masu kai zuciya nesa a duk lokacinda wani abu ya shiga tsakaninsu.
Alhaji Bello yace manoma da makiyaya su sanifa su yan uwan junane don haka bai kamata ace ana samu ta kaddama a tsakaninsuba. Saboda haka ya kamata sukasance masu doka da ka ididin noma da kiwo a koda yaushe.
Bello ya kuma kara da cewa sun tattauna da kwamandan rundunan tsaro farin kaya wato civil defence na jahar Adamawa dangane da mataken da za a dauka domin dakile dukkanin matsaloli da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya a fadin jahar baki daya.
Ya kuma kirayi gwamnatin da ta taimaka wajen shiga tsakani wajen samarwa makiyayan wadaceccen burtali wanda haka zai taimaka wajen kawo karshen rikici a tsakanin manoma da makiyaya.
Comments
Post a Comment