Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta dauki dukkanin matakai domin bada kariya alokacin bukukuwarBabban Sallah.

Runduna yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin bada kariya ga al umma musulmai domin ganin an gudanar fa bukukuwar Babban Sallah lafiya ba tare da matsalaba. Kakakin runduna yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ba baiyana haka a yayinda ake daf dafara bukukwar Babban sallah na wannan shekara. Sanawar dai nacewa anjiyo kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola nacewa rundunan ta dauki dukkanin matakai da ya kamata domin bada kariya a wurare bukukuwar dake sasssa daban daban a fadin jahar. Don haka nema kwamishinan ya umurci mataimakinsa mai kula da sashin aiyuka da yayi dukkanin abinda suka dace domin tabbatar da cewa komai ya gudana cikin kwanciuar hankali musammanma a wuraren da za a gudanar da sallar idi a fadin jahar ta Adamawa baki daya. Har wayau rundunan tasha alwashin saka kafar wando daya ga duk wanda kekokarin karya doka ko kuma yiwa doka Karen tsaye domin rundunan baza ta lamicewa duk wanda ya karya dokaba. Da wannan nema rundunan ke kira ga dukacin al ummar jahar da sukasance masu taimakawa rundunan da wasu bayanain sirri da zai baiwa rundunan damar dakile aiyukan ta addanci. Rundunan ta kuma taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan bikin Babban sallah dama al ummar jahar ta Adamawa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE