An gudanar da gasan karatun Al kur ani mai girma a tsakanin marayu a jahar Adamawa.

A karon farko an shiryawa maru gasara karatun Al kur ani mai girma domin ganin an samu cigaban karatun Al kur ani a tsakanin Al umma. Da yake jawabi a wurin bikin rufe gasara karatun Al kur ani wanda aka gudanar a makarantar FOMWAN dake yola. Mallam Musa Kaduna yace wannan shine karo na farko kenan aka shirya irin wannan gasar ga marayu domin ganin an karawa marayun kwarin gwiwar haddar karatun Al kur ani mai girma. Shima a jawabinsa bako mai jawabi Mallam Ali Mamman ya baiyana ahirya irin wannan gasa yana da matukan muhimmanci da wannan nema yake kira ga mawadata da suyi koyi da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi wajen taimakawa marayu, wanda avewarsa hakan zai kara musu kwarin gwiwar cigaba da karatu yadda ya kamata. Shugaban taron wato Dr Abdullahi Basullube kirayayiwa mawadata da sukasance suna tallawa iyayen marayun domin su samu damar daukan dawainiyar marayun domin su amfani Al umma. Shikuwa hakimin Nasarawi Abba Alhaji Abubakar Aliyu Mustafa shawartan mahalarta taron yayi da su kara zage damtse wajen taimakawa marayun a koda yaushe domin su samu kyakkawar kula, da ilimi harma da samar da zaman lafiya a tsakanin Jama a. Da yake jawabi ko odinatan shirya gasar Muhammed Auwal Aytan yace dalube 72 ne wadanda suka fito daga kananan hukumomi aahirin da daya dake fadin jahar ta Adamawa ne suka ahiga gasar. Wadanda sukayi zarra a gasar sune zau wakilci jahar ta Adamawa a wurin gasar na kasa da za a gudana a jahar Filato a ranan 28-8-2023. Kawo yanzu da wadanda sukayi nasaran cingasara sun hada Zakariya Usman Raji dan shakara 18 wanda ya fita daga karamar hukumar yola ta kudu. da Aisha Muhammed Suleiman yar shekaru 15 wadda ta fito daga karamar hukumar Demsa wadda kuma sune zasu wakilci jahar ta Adamawa a gasar ta kasa a jahar Filato.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE