Cibiyar bunkasa harkokin harsuna da Al adu a Najeriya ta kawo karshen shirye shiryenta na shekara ta 2023.

Cibiyar bunkasa harsunan Najeriya ta kasa NICO tace ta kammala shirye shiryenta na shekara ta 2023 dangane da gangamin wayarwa al umma kai dangane da harsuna a jahar Adamawa.
An dai gudanar da bikin kammala shirye shiryen ne a Barikin yan sanda dake nan yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Darektan cibyar ta NICO a shiyar Arewa masau gabas Mrs Jane Anigala wanda shugaban sashin gudanarwar cibiyar Abdullahi Ndribita ya wakilta yace tun a ahekara ta 2017 ne cibiyar ta fara gangamin wayarwa jama a kai dangane da harsunan a Najeriya.
Ya kuma baiayana cewa cibiyar na da shiyoyi har sha shida a shiyoyi ahida dake fadin Najeriya.harma da birnin tarayya Abuja. Abdullahi ya baiyana damuwarsa dangane da yadda ake samun koma naya a bangaren cigaban harsunan Najeriya kuma abun takaicinma shine yadda wasu iyaye basu koyawa yaransu harsunansu, wandama hakan ya sa wasu matasa basa alfahari da magana da harshensu acewarsa matasa su sani basu da abun tunkaho ya wuce harshensu.
Ya ce harshe yana daga cikin abunda zai kawo cigaban dama bunkasa al adu a tsakanin al umma baki daya. Darektan ta kuma shaidawa wadanda suka halarci taron cewa koyon sabon harshe abune da yake da wajalar gaske din haka akwai bukatan a maida hankali wajen yin magana da harshen a Koda yaushe domin samun cigaba yadda ya kamata. Shima anashi jawabi kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Wanda Area Kwamandan karewa ACP Ishaya Umar Muhammed ya wakilta ya baiyana cewa shirya irin wannan gangami dangane da harsuna zai taimaka wajen hadin Kai dama taimakawa wajen yaki da aikata laifuka baki daya.
NAFAN COLLEGE OF SCIENCE AND HEALTH TECHNOLOGY Kwalejin dake haras da kiwon lafiya kimiya da fasaha dake Unguwar Jambutu a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwalejin ta bude tare da fara karantar da kwasakusai a bangarorin kiwon lafiya daban daban da suka hada da: 1. Pharmacy Technician (PT). 2. Health Information Technician (HIT). 3. Medical X-Ray Technician (X-Ray). 4. Junion Community Health Extension Worker (JCNEW). 5. Medical Laborotary Technician (MLT). 6. Dental Surgery Technician (DST). 7. Community Health Extension Worker (CHEW). 8. Public Health Assistant. 9. Public Health Technology (HND) 10. Health Information Technology 11. Social Welfare. 12.. Nutrition and Dietetics. 13. . Public Health Technician. Domin samun damar shiga kwalejin ko sayan takardan shiga kwalejin sai a ziyarci jarabar kwalejin dake Jambutu ko a tuntubi wadan nan lambobin waya kamar haka: 07989481034 da 07038466510 ko 08142680500. Muna maraba da zuwanki a Koda yaushe Kuma ashirye muke mu biya muku bukatunku a Koda yaushe sai kunzo.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE