Gwamnan jahar Adamawa ya shiga tsakanin domin kawo karshen ta kadda dangane da wasu kalamai da wani malami a jahar Bauchi.
Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri tare da malamai addinin musulunci sunyi zaman tattaunawa domin kawo karshen cece kuce da ta faru a tsakanin malamai da malamin addinin musulunci dake jahar Bauchi Dr AbdulAziz Idris Dutsen Tanshi.
Tunda farko dai gwamna Umaru Fintiri sunyi ganawar sirri da malamai da suka hada da Sheikh Abdullahi Bala Lau Sheikh Kabiru Gombe Sheik Abdulwahab Kano tare da gwamnan jahar Bauchi gwamna Bala Muhammed a gidan gwamnati daka jahar Bauchi.
Da yakeyiwa manema labarai jawabi bayan fitowarsu da taron gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace sun kasance a gidan gwamnatin ne domin tattaunawa da kuma samar da masalaha dangane da furucin mallam Dr AbdulAziz Idris yayi lamarin da ya janyo martani masu zafi a fadin Najeriya.
Gwamna Fintiri ya kuma yabawa gwamna Bala Muhammed na jahar Bauchi bisa kokarinsa na wanzar da zaman lafiya a fadin jahar.
A jawabinsa gwamna Bala Muhammed yace yakamata a rinka taka tsantsan dangane da addini ya kuma gidewa malamai dama gwamnan jahar Adamawa bisa na mijin kokari da sukayi na kawo karshen matsalar.
Taron ya samu hakartan kwamishinan yan sandan jahar Bauchi Musa Muhammad Auwal da darekta hukumar tsarin farin kaya DSS Hussaini Abdullahi da Babban Alkalin jahar Mai shriya Rabi u Talatu Umaru, da wakilain darikar Tijjaniya da dai sauransu.
In za a iya tunawa dai a kwanakin bayane Dr Idris Abdul Aziz yayi wasu malamai dangane da mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Wanda hakan ya haifar kace nace a tsakanin malamai dama al umma.
SANRWA. SANARWA. SANARWA
Hukumar makaramtar NA IBI ACADAMY dake Damsawa a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Tana garin cikin sanar da Al umma cewa ta fara sayar da Form din shiga makaramtar daga matakin Firamaer da sauransu. Kuma makarantar ta shahara wajen karantar da bangarori da dama da su hada na addini dama na zamani. Kamar haka.
A bangaren addini ana karantar da haddan Al ku ani Maigirma, Nahaw, Tauhid, Luggatul Arabiya, da dai sauransu.
A bangaren Boko kuwa makarantar na karantar da darasin lissafi wata Maths da harshen turanci English, Computer, Social Study, Agriculture, da dai Sauransu.
Ana zuwa makarantar cikin kwanaki biyar wato daga litinin zuwa Jumma a Kuma ana fara karantarwane daga karfe bakwai na safe zuwa karfe hudu da rabi na yamma a kowace tana. Bugu da Kari makarantar na ciyar dalube abinci sau daya a rana sannan akwai motocin debo dalube da Kuma mayar dasu gidajensu kana akwai masu kula da dawainiyar dalube a cikin makarantar ta NA IBI ACADEMY .
Domin karin bayani ko sayan Form din sai a ziyarci harabar makarantar dake dake Damsawo ko a tuntubi Number wayoyin waya kamar haka. 07063516642.
08024772558.
Sai kunzo
Comments
Post a Comment