Kungiyar kwadigo a Najeriya ta bugi kirjin shiga yajin aikin kasa baki Daya.
Gwamnatin tarayya da wakilan kungiyoyin kwadago za su sake ganawa a ranar litinin din nan domin sake lalubo mafita aka tankiyar da ke tsakaninsu.
Kungiyar ta kwadago ta na shawarta alummar Najeriya su tanadi Abinci da magunguna da sauran Kayan amfanin yau da kullum saboda yajin aiki da za a tsunduma na tsawon mako guda saboda cire tallafin man fetur.
Ta ce wannan gargadi ya zama wajibi saboda yajin aikin zai dakatar da duk wasu mahimman ayyuka da suka hada da zirga zirgar harkokin sufuri da makarantu da bangaren kula da lafiya, da kasuwanci da sauran Ayyuka masu mahimmanci.
Mataimakin shugaban kungiyar na kasa Chris Onyeka, ya tabbatar da haka a lokacin da yake magana da manema labarai a Abuja, inda ya ce akwai Bukatar Yan Najeriya su takaita zirga zirgansu saboda kaucewa duk wata cikas da za su iya fuskanta.
Yace ungiyar su ta baiwa Gwamnatin tarayya waadin kwanakin 7 , Wanda waadin zai kare daga ranar Laraba,2 ga watan Agusta na 2023, a cikin wata sanarwa data sami sa hannun shugaban kungiyar ta kasa John Ajaero, ta zargi gwamnatin tarrayya a karkashin jagorancin shugaban kasa BOLA Tinubu da gazawa wajen cimma matsaya a alkawarinda suka yi tun da farko
SANARWA. SANARWA SANARWA
Hukumar makaramtar NA IBI ACADAMY dake Damsawa a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Tana garin cikin sanar da Al umma cewa ta fara sayar da Form din shiga makaramtar daga matakin Firamaer da sauransu. Kuma makarantar ta shahara wajen karantar da bangarori da dama da su hada na addini dama na zamani. Kamar haka.
A bangaren addini ana karantar da haddan Al ku ani Maigirma, Nahaw, Tauhid, Luggatul Arabiya, da dai sauransu.
A bangaren Boko kuwa makarantar na karantar da darasin lissafi wata Maths da harshen turanci English, Computer, Social Study, Agriculture, da dai Sauransu.
Ana zuwa makarantar cikin kwanaki biyar wato daga litinin zuwa Jumma a Kuma ana fara karantarwane daga karfe bakwai na safe zuwa karfe hudu da rabi na yamma a kowace tana. Bugu da Kari makarantar na ciyar dalube abinci sau daya a rana sannan akwai motocin debo dalube da Kuma mayar dasu gidajensu kana akwai masu kula da dawainiyar dalube a cikin makarantar ta NA IBI ACADEMY .
Domin karin bayani ko sayan Form din sai a ziyarci harabar makarantar dake dake Damsawo ko a tuntubi Number wayoyin waya kamar haka. 07063516642.
08024772558.
Sai kunzo
Comments
Post a Comment