Majalisar dattawar Najeriya tayi watsi da bukatan wani sanata kan sake Nmandi Kanu.

Majalisar dattawar Najeriya tayi watsi da batun nan da wani sanata da ya fito daga yankin kudu masau gabas ya nemi da asako shugaban kungiyar IPOB Nmandi Kanu. Sanata mai wakiltan Imo ta yamma sanata Osita Izunaso ne dai ya gabatar da batun inda yace sakin Nmandi Kanu zai taimaka wajen kawo karshen zaman gida da yan kungiyar suka tilas tawa All ummar jahar . A Cewarsa dai tilasta zaman gidan ya gurgunta harkokin kasuwancin yankin, dama tsadar rayuwa harma da dakile tattalin arzikin yankin baki daya. Sanatocin sunki amincewa da bukatan da dan majalisar ya gabatar ne tare ta shaida masa da ya sanarwa gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan wadannan kungiyar tare da tsare duk wanda ya karya doka. Tun a shekara ta dubu biyu da ashirin da daya ne dai wasu yan binga suka tilastawa jama a zaman gida duk da cewa kungiyar ta IPOB ta nisanta kanta daga lamarin. Yanzu haka dai shugaban kungiyar ta IPOB wato Nmandi Kanu yana tsare a yayinda ake cigaba da masa shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE