Majalisar dokokin jahar Adamawa ta karbi sunayen mutane 23 domin tantancesu a matsayin kwamishinoni

Majalisar dokokin jahar Adamawa a ranan alami da ta ganatane dai ta karbi sunayen mutane ashirin da uku domin tantancesi domin basu mukamen kwamishinoni a jahar Adamawa. Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ne ya mikawa majalisar sunayen kwamishinoni inda gwamnan ya bukaci Yan majalisar da su tantancesu a matsayin Yan majalisar zantarwar jahar.
Da yake karban sunayen kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Hon.Bathiya Wesley a yayinda ya jagoranci zaman majalisar yace zasu zasuyi maganar ranan da zasu tantance sunayen.
Mutane ashirin da uku da aka mika sunayensu dai sun hada da Barr Wali Yakubu daga Madagali sai Dr John Ishaya Dabari da Mery Augustina Vasumu daga Michika sai Hon. Usman Abdullahi daga Mubi ta kudu da Tijjani Maksha daga Maiha. Dr Umar Garba Pella daga Hong. Farfesa Fintiwa David Jatau daga Gombi. Abdullahi AdamuPrambe daga Song.
Sauran sun hada Job Haggai Sama daga Girei. Ibrahim Mijinyawa Yayaji daga yola ta arewa. Barr Bello Hamman Diram daga yola ta kudu chief Felix Tangwami da Hon. Iliya James daga Demsa. Ibrahim Haruna daga Shelleng da Hon. Kallamu Musa Muhammed daga Mayo Belwa. Adamu Atiku Jada. Aloysius Babadoke Jada Sai Kuma Emmanuel Biridimso Toungo. Mrs Nedo Geoffrey Numan Titus Solomon Lamurde Anthony Birina Guyuk. Muhammed Sadiq Ganye. Ayuba Audu Tanko Mubi ta arewa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE