Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar yola ta arewa takudiri aniyar koyarwa yaran sanin watannin addinin Musulunci.

majalisar harkokin addinin musulunci a karamar hukumar yola ta arewa ta sha alwashin ganin ta wayarwa dalube Kai dangane da sanin watannin addinin musulunci dama shekaran. Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a yola ta arewa Alhaji Abdullahi Abubakar Butu ne ya baiyana haka a lokacinda yake amsa tambatoyi daga manema a yola. Alhaji Abdullahi Butu yace yanzu haka suna Shirin rarrabawa makarantun Islaniyoyi takardu wadanda suke dauke da watannin addinin musulunci dama kalandar ta addinin musulunci. A cewarsa dai karantar da yara sanin watannin addinin tun suna matakin islamiya zai taimaka wajen wayarwa jamma a Kai dangane da watannin na addinin musulunci. Ya Kuma kirayi iyayen da Suma su bada tasu gudumawar wajen fahintar da yaran sanin watannin addinin musulunci tun suna yara domin samun cigaban addinin musulunci.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE