Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ya tabbatar da kama mutane 25 wadanda ake zargin da hanu a kwashe kayakin abinci a rbunan gwamnati.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da kama tare da tsare mutane a kalla ashirin da biyar Wanda ake zargi da hanu a cikin fasa tare da kwashe kayakin abinci dama sauran kayakin a runbun a abincin na gwamnati jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar ta Adamawa SP Suleiman Yahay Nguroje ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a yola. SP Suleiman Yahaya Nguroje yace rundunan satayi dukkanin maiyiwa domin maido da dkkanin kayakin da aka sace.
SP Suleiman ya kuma tabbatarwa al ummar jahar Adamawa cewa rundunan zatabi dukkanin ka idodi da suka dace kamar yadda gwamnatin jahar ta baiyana amman kuma jama a su sani rundunan zata shiga kafar wando daya da duk wanda yayiwa doka karen tsaye. A nashi bangaren Shuguban hukumar agajin gaggawa ta kasa dake jahohin Adamawa da Taraba Landan Ayuba ya baiyana damuwarsa dangane da gungun matasa da suka gudanar da irin wannan barna ya kuma kirayi hukumomi da sukasance masu inganta tsaro a runbunan gwamati.
Ya kuma shaidawa matasan cewa su sani wannan lamari da suka aiwatar bai daceba don haka su nisanta kansu daga duk abinda zaikawao tashin hankali a tsakanin al umma.
SANARWA. SANARWA. SANARWA Hukumar makaramtar NA IBI ACADAMY dake Damsawa a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Tana garin cikin sanar da Al umma cewa ta fara sayar da Form din shiga makaramtar daga matakin Firamaer da sauransu. Kuma makarantar ta shahara wajen karantar da bangarori da dama da su hada na addini dama na zamani. Kamar haka. A bangaren addini ana karantar da haddan Al ku ani Maigirma, Nahaw, Tauhid, Luggatul Arabiya, da dai sauransu. A bangaren Boko kuwa makarantar na karantar da darasin lissafi wata Maths da harshen turanci English, Computer, Social Study, Agriculture, da dai Sauransu. Ana zuwa makarantar cikin kwanaki biyar wato daga litinin zuwa Jumma a Kuma ana fara karantarwane daga karfe bakwai na safe zuwa karfe hudu da rabi na yamma a kowace tana. Bugu da Kari makarantar na ciyar dalube abinci sau daya a rana sannan akwai motocin debo dalube da Kuma mayar dasu gidajensu kana akwai masu kula da dawainiyar dalube a cikin makarantar ta NA IBI ACADEMY . Domin karin bayani ko sayan Form din sai a ziyarci harabar makarantar dake dake Damsawo ko a tuntubi Number wayoyin waya kamar haka. 07063516642. 08024772558. Sai kunzo

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE