Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace tana tsare da mutane sama da dari wadanda ake zairgi da wawushe kayakin abinci.
Runduan yan sandan jahar Adamawa tace ta kama mutane da dama wadanda ake zargi da hanun a cikin wawushe kayakin abincin gwamnati dana al umma.
A wata sanarwa da kakakin runduna yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya aikewa manema labarai a yola, na cewa rundunan ta samu nasaran kama mttane akalla dari da goma (110) wadanda ake zargi da faffasa runbuna Adana abincin gwamnati tare da kwashe kayakin.
Da wannan ne rundunan ke gargadi al umma da su kaucewa dukkanin abinda zai haifar da matsaloli a tsakanin Al umma.
A cewar kakakin rundunan yan sandan rundunan a shirye take ta saka kafar wando daya da duk wanda yayiwa doka karan tsaye.
Comments
Post a Comment