A yau ne gwamnan jahar Adamawa zai rantsar da kwamitin rabon tallafi
Gwamnatin jahar Adamawa tace zata rantsar da komitin raba tallafi a yau laraba 22 ga wata sabanin ranar alhamis 23 ga watan agusta da ta sanar a can baya.
Za a kuma yi bukin kaddamarwan ne a dakin taro dake gidan gwamnati a birnin Yola.
Sauyin ranar dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarun gwamna, Humwashi wonosikou ya aike wa manema labaru.
sanarwan ta kuma umurci Komitin rabon tallafin wanda ya kunshi mutum 20 karkashin shugaban cin sakataren gwamnatin jaha, Auwal Tukur da su hallaru da karfe tara da rabi na safiya.
Gwamnan jaha Ahmadu Umaru Fintiri ya kuma bada umirnin cewa mambobin komitin su tabbatar da adalci yayin rabon tallafin tare da la'akari da manufar gwamnati na kula da jin dadin yan jahar.
Har wayau a ranar laraban za a rantsar da sabon mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labaru, Baba Yola Toungo da zaran an kammala rantsar da mambobin komitin raba kayakin tallafi.
Comments
Post a Comment