An baiyana cewa hanyoyin sadarwa suna da muhimmanci a bangaren jinkai.

Inganta harkokin sadarwa ne Ka dai zaitaimaka wajen bada agajin gaggawa ta yin amfani da kafafen yada labarai. Manajan aiyuka na BBC media action Nicolas Raul ne ya baiyana haka a lokacin kammala horo da akayiwa kafafen yada labarai da masu aiyukan jinkai a jahar Adamawa Nicolas Raul yace sama da shekaru ashirin bbc media action tana aiyukan taimakawa mutane da suke da bukatar agaji biyo bayan hali da suka shiga sakamokon rikici. Ya Kuma kara da cewa sadarwa yana taka muhimmiyar rawa wajen aiyukan jinkai don haka ne ma suka shiryawa kafafen yada labarai da masu aiyukan jinkai wadanda suka fito daga jihohi Adamawa da Borno hora na musamman domin samun cigaba Wanda ya jagoranci horaswa na BBC media action Deji Arosho da Sumayya Ibrahim Yusuf sun gabatar da kasidu masu taken akwai bukatar inganta sahin sadarwa domin sadarwa Yana daga cikin aiyukan jinkai Sun Kuma baiyana cewa akwai bukatar hada Kai da kowa domin Suma su bada tasu gudumawa wajen aiyukan jinkai. Shima anashi jawabi Muhammed Sani Bello Wanda Yana Daya daga cikin masu horon na BBC media action yace yayata karya Yana haifar da matsàloli da dama don haka nema yakirayi mahalarta bitan da su tabbatar sun tantance labarai kafin su yadashi ga Al umma. Wadanda aka horas din dai sun fito daga kafafen yada labarai daban daban dake jihohin Adamawa, da Borno.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE