An baiyana cewa shayar da jarirai nonon uwa Yana da mutukan muhimmanci. Malama Jummai

An shawarci iyaye mata musammanma masu shayarwa da su maida hankali wajen baiwa jariransu mama Akai akai domin ganin sun samu cikekken lafiya da Kuma kuzari a Koda yaushe. Malama Jummai Wycliffe kwararriya a fannin mata masu dauke da Juna biyu da Kuma shayarwa a asibitin kwararru dake yola, ne ta bada wannan shawara a zantawarta da Jarida Al Nur Hausa dangane da watan shayar da jarirai nonin uwa ta duniya. Malama Jummai tace shayar da jarirai nonon uwa Yana da tasiri sosai domin Yana baiwa jarirai kariya daga cututtuka daban daban, ga koshin lafiya, da Kuma Kara son Juna a tsakanin uwa da jarirai. Da wannan nema ta kirayi magudanta da sukasance suna baiwa mata masu shayarwa kula sosai da karamusu kwarin gwiwa wajen shayar da jarirai yadda ya kamata. Ta Kuma shawarci mazaje da sukasance suna baiwa mata musammanma wadanda ke dauke da Juna biyu kyakkawar kula har su haifu, da Kuma basu isshesshen abinci dama kwantar musu da hankali Wanda acewarta hakan zai taimaka wajen Samar musu da ruwan manarsu sosai, Jummai ta Kuma baiyana cewa shayar da jarirai nono na tsawon watanni shida na farkon haifuwar jarirai abune da yake da mutukan muhimmanci domin nonon Yana dauke da sanadarin abinci da ruwa. Don haka nema da zaran an hafi yaro da Sa a Daya ya kamata a fara bashi nono kasancewa Shan farko da zaiyi nonon zai fara fitar da ruwane Don haka nema hukumar kiwon lafiya ta duniya ta aiyana watan takwas da ya zama watan fadakarwa dangane da shayar da jarirai nonon uwa. Malama Jummai tace suna fuskantar kalu bale da dama da suka hada da rashin fahinta da wasu basayi da Kuma kararanci wayar da Kai dangane da shayar da nonon uwa. Tace mazama suna da rawa da zasu iya takawa wajen shayar da jarirai ta hanyar baiwa masu shayarwan hadin Kai da goyon baya da kwarin gwiwar ta basu kulawa da kwantar musu da hankali domin ganin sun samu damar shayarwa yadda ya kamata. Tace cin ingancaccen abinci da samun kwanciyar hankali Yana taimakawa wajen baiwa mashu shayarwa cikekken samun lafiya da Kuma samun wadaceccen ruwan mama ga uwa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE