An bukaci baiwa gwamnati da kwamitin rarraba kayakin tallafi hadin Kai a jahar Adamawa.
jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintir ta kudiri aniyar taimakawa al ummar jahar domin rage radadin wahala da ake ciki biyo bayan cire tallafin mai fetur wanda gwamnatin tarayya tayi.
Mai taimakawa gwamna fintiri na musamman kan harkokin jama a Barista Sunday Wugira ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola.
Barista Sunday yace tuninma aka sayar da taki da yakai tirela ashirin cikin farashi mai rafusa ga manoma dake fadin jahar. Wanda kuma an dauki matakin hakane domin bunkasa harkokin noma a fadin jahar domin samun saukin kayakin abinci a fadin jahar.
Barista Wugira yace da yardan Allah nan gaba kadan za a kawo tirelar masara hamsi dana shinkafa ashirin domin ganin an samawa al ummar jahar saukin rayuwa da kuma rage radadin kuncin rayuwa da al ummar suka tsinci kansu a ciki.
Barista ya kuma baiyana cewa a bangaren sufirima gwamnatin jahar ta Adamawa ta sayo manyan motocin safa guda goma wadanda tuninma suka iso fadar ta jahar Adamawa a wani mataki na samun saukin sifiri a fadin jahar.
A cewarsa dai gwamnati ta tashi tsaye domin ganin al ummar jahar sun samu waraka da kuma mare romon domukiradiya da kuma samun kauciyar hankali.
Don haka nema Barista Sunday ya bukaci da al ummar jahar su kasance masu baiwa gwamnati dama kwamitin da zai kula da rarraba tallafin hadin kai da goyon baya domin ganin an cimma burin tallafawa yadda ya kamata.
Ya kara da cewa kwamtin rarraba kayakin tallafin na nan a shirye domin ganin an gudanar da rabon kayakin yadda ya kamata ba tare da wasu matsaloliba saboda haka yana da kyau a baiwa kwamitin hadin kai damin ya samu damar rarraba kayakin cikin kwanciyar hankali.
Ya kuma shawarci daukacin al ummar jahar ta Adamawa da sukasance suna yiwa gwamnati adu a dama jahar harma da kasa baki daya. Domin neman taimakon Allah ma daukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro da ake fama dashi.
Ya kuma bukaci da al umma musammanma matasa da su maida hankali wajen neman sana o i dogaro da kai wanda acewarsa haka zai taimaka wajen samun cigaba harma da bunkasa tattalin arzikin jahar baki daya.
Don haka mutane sukasance masu hakuri da kuma taimakon juna a koda yaushe domin samun hadin kai a tsakanin al ummar jahar ta Adamawa baki daya.
Comments
Post a Comment