An bukaci masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin samarwa manoma sauki.

An kirayi masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin ganin an samu rangwame a bangaren maifetur saboda samarwa manoma saukin gudanar da harkokinsu tadda ya kamata. Shugaban kungiyar manoma Yakkore dake Jambutu Alhaji AbdulRazak Abubakar ne ya wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji AbdulRazaka yace tsadar maifetur yana gurgunta aiyukan noma sosai saboda haka ya zama wajibi su kirayi masu ruwa da tsaki da su taimaka su shiga tsakanin domin warware matsalolin baki daya. AbdulRazak ya Kara dacewa manoma a jahar Adamawa musammanma kananan manoma suna fuskantar kalubale da dama da suka hada da rashin taki, magungunan feshi, da dai sauransu, wanda kuma acewarsa hakan na haifar da koma baya a bangaren noma. Da wannan ne yake kira ga gwamnatin tarayya dana jahar da suyi dukkanin abunda suka dace domin ganin manoma sun samu saukin gudanar da aiyukansu, domin samar da wadaceccen abinci, samar da aikiknyi, harma da bunkass tattalin arzikn jahar dama kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.