An kirayi Shuwagabani da sukasance masu adalci.

An kirayi shuwagabani a dukkanin matakai da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa adalci da gaskiya da rikon amana domin samun tsira ranan gobe kiyama. Sanannen malamin addinin musuluncin nan Sheirk Dr Sani Rijiyar Lemo ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin taron kwamitin Da awa na mata ta kasa da aka gudanar a jahar Gombe. Sheirk Sani Rijiyar Lemo yace ya kamata shuwagabani sukasance masu sanya tsaron Allah Madakakin sarki a zukatansu domin ganin sunyi adalci a ahugabancinsu.
Da take jawabi a wurin taron uwar gidan mataimakin ahugaban kasa Hajiya Nana Kashim Shettima wanda uwar gidan gwamnan jahar Borno Hajiya Falmata Babagana Zulum ta wakilta ta baiyana cewa mata sune na gaba gaba wajen yiwa yara tarbiya na gari. Ta kuma kirayi kwamitin mata masu Da awa da su hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin magance matsalar shaye shaye a tsakanin matasa domin samun ahuwagabani na gari.
Anata jawabi uwar gidan tsohon mataimakin shugan kasa Hajiya Amina Namadi Sambo ta baiyana jindadinta dangane da wannan taro da women in Da awa suka shirya wanda acewarta wannan ya nuna cewa za acigaba da gudanar da Da awa domin cigaban addinin musulunci tare dayi musu adu ar Allah ya saka musu.
Ta kuma kirayi al umma da sucigaba dayiwa kasa adu o i samar da zaman lafiya da kuma magance kalu balen tsaro a fadin Najeriya baki daya. Itama uwar gidan gwamnan jahar Gombe Hajiya Asma u Inuwa Yahaya wanda Hajiya Habiba Abubakar ta wakilta kiran mata tayi da su marawa kwamitin women in Da awa baya domin magance matsaloli da ake fuskanta.
Taron dai ya samu halartar daukacin membobin kungiyar daga jihohi dake fadin kasan nan tare da malamai sarakunan gargajiya manyan Jami an gwamnati da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE