An rantsar da kwamitin da zai gudanar da rabon tallafi wa jama a domin rage radadin wahala sakamokon cire tallafin maifetur

Gwamnan Jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci mambobin komitin tsarawa da rabon tallafi na jaha da su guji son kai yayin gudanar da aikin da aka daura musu. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya mika wannan bukata ne a ranar laraba yayin kaddamar da komitin rabon tallafin mai mabobi 22 wanda aka yi a dakin taro dake gidan gwamnati a birnin yola. Gwamna Fintiri wanda mataimakiyar shi, farfesa Kaletapwa George Faruta ta wakilta yayin kaddamar wan yace al’ummar jahar Adamawa na fama da wahalhalu sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin taraiya ta yi, inda gwamnatin jahar ta yanke shawarar bullo da wasu matakai da za su taimaka gurin rage radadin, hakan ya sa ake bukatan komiti wanda babu son kai ko ma wani iri ne.
Gwamnan yace an daura wa komitin hakkkin bullo da dukkan dabaru da ake bukata na zirga zirgan kayakin tallafin daga ma’ajiya zuwa inda za a gudanar da rabon, da kuma sa ido tare da tuntuban masu ruwa da tsaki da ke cikin al’umma domin tabbatar ta yin adalci gurin rabon zuwa wadanda ake sa ran rabawa a kananan hukumomi ashirin da daya na jaha. GwamnamAhmadu Umaru Fintiri ya kara da cewa a hada da duk wani kungiya ko mutum da ke da amfani domin tabbatar tda nasarar wannan rabiya. Da yayi jawabi a madadin mambobin komitin, shugaban kuma sakataren gwamnatin jaha, Auwal Tukur ya gode wa Allah tare da godewa gwamnan da ganin cancantan su gurin aiwatar da wannan aiki. Auwal Tukur yace mambobin komitin sun hada da mutane masu kima daban daban wanda ke da niyyar aiki tare domin ganin an raba wadannan tallafi bisa adalci. Komitin rabon tallafin dai sun hada da sakataren gwamnatin jaha a matsayin shugaba, sai sarakunan gargajiya biyu wato Amna Shelleng da Hama Bachama, sai mambobin majalisar taraiya daga jahar Adamawa guda biyu, sai kuma mambobin majalisar dokokin jaha guda biyu, da komishinan ma’aikatan gyare gyare, hade al’umma da jinkai, da komishinan noma, shugaban ma’aikatan jahar Adamawa, shugaban shugabannin kananan hukumomi na jaha wato ALGON, da komishinan yan sanda, briget komanda da komandan dakarun sojin sama a matsayin mambobi.
Sauran sun hada da daraktan DSS na jahar Adamawa, komandan dakarun tsaron farin kaya na civil defence, kungiyoyin CAN, Muslem kansil, NUJ, TUC, NCWS da kuma majalisar matasa wato NYCN, sai kuma ADSEMA a matsayin sakatariyar rabon.
A DAYA BANGAREN KUMA MAJALISAR ZANYARWAN JAHAR ADAMAWA TA AMINCE DA SAYO MOTOCI KIRAN BASBAS A WANI MATAKI NA KAWO SAUKIN SIFIRI A FADIN JAHAR. Gwamnatin jahar Adamawa ta amice da sayo manyan motoci basbas masu kujeru 58 guda goma a matsayin tallafi domin rage wahalhalun zirga zirga ga al’ummar jahar ke fama da shi. Hakan na kunshi ne cikin jerin matsaya da majalisar zantarwan jahar ta cinma a zaman ta na laraba 22 ga watan agustan 2023 , wanda mataimakiyar gwamna, Farfesa Kaletapwa Farauta ta jagoranta. Yayin da tayi wa yan jarida jawabi jim kadan bayan kammala zaman majalisar komishiniyar yada labaru, Neido Kufulto ta ce gwamnati zata sayo motoci masu gujeru 58 guda 10 a kan kudi naira biliyon daya da miliyon sittin daga kamfanin kirar motoci na INNOSUN. Komishiniyar ta ce sayo wadannan manyan bas bas din zai taimaka matuka gurin shawo kan kalubalen zirga zirga da yan jahar ke fama da shi sakamakon cire tallafin mai. A cewar ta, motocin za su rika zirga zirga ne akan farashi mai rahusa domin amfanar al’ummar jaha. Majalisar ta kuma amince da sayo hatsi wanda zata sayar wa yan jahar a farashi mai rahusa. Gwamnati zata sayo hatsin daga gurin manoma ta kuma sayar wa al’umma a kan farashi mai sauki. Gwamnatin jahar ta kirayi al’ummar ta da su kara hakuri tare da zaman lafiya da juna ganin itama tana nan tana kokarin ta domin ganin ta samar da tallafi da za su rage radadin da ake ji, tare da kira ga al’umma da su shirya domin noman rani ganin lokacin ya sako kai. Gwamnatin ta kuma yi amfani da wannan dama gurin kira ga wadanda ke da zama a hanyoyin ruwa da su haura tudu domin gujewa ambaliya ko ma wani yanayin gaggawa da zai ba da wahalan shawo kai

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE