An shawarci gwamnatin tarayya Dana jihohi da su Kara kaimi wajen dakile rikici a tsakanin manoma da makiyaya.
An kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su kara kaimi wajen daukan matakin kawo karshen rikici a tsakanin makiyaya da manoma a fadin Najeriya baki daya.
Shugaban kungiyar Sullubawa ta kasa shiyar jahar Adamawa Alhaji Bello Ardo ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola.
Alhaji Bello Ardo ya yabawa gwamnatin tarayya dana jihohi bisa kokari da sukeyi na warware matsaloli dake faruwa a tsakanin manoma da makiyaya a fadin Kasan nan don haka akwai bukatar su kara himma wajen dakile matslar baki daya. Don farfado da tattalun arzikin, samar da zaman lafiya cigaban a jahar dama kasa baki daya.
Ya kuma kirayi hwamnatin tarayya dana jihohin da cewa in har zaau kafa kwamiti dangane da abinda ya shafi manoma da makiyaya to ya kamata su hada da shuwagabanin makiyaya dana manoma wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kawar da rikici a tsakanin manoma da makiyaya.
Alhaji Bello ya kuma kirayi masu ruwa da tsaki da ma hukumomin tsaro da sukasance masu hada kansu da kuma yin aiki tare domin ganin ba a rinka samun tashin hankali a tsakanin manoma da makiyayaba.
Harwayau ya yabawa kwamandan rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula a jahar civil defence Ibrahim mai Nasara wanda shima yana taka rawan ganin wajen dakile rikici a tsakanin manoma da makiyaya.
Rikici a tsakanin manoma da makiyaya dai ya dade ya ciwa gwamnati tuwo. a kwarya lamarinda kanyi sanadiyar asaran rayuka da dama da muhallai dama dukiyoyi masu yawa.
Comments
Post a Comment